Jagoran jam’iyyar adawar Succes Masra, shi ne ya sanar da ɗaukar wannan mataki a lokacin da yake gabatar da jawabi ga magoya bayansa a birnin Ndjamena.
“Shiga wannan zaɓe, a yau kuma a cikin wannan yanayi, na nufin cewa mun amince da kafa tsarin wariya a cikin kasarmu, ma’ana dai tamkar mun yarda da sakamakon da tuni aka wallafa a cikin kwamfutar abokan hamayyarmu ne” a cewar Masra
Succes Masra ya buƙaci a ɗage wannan zaɓe saboda ambaliyar da ake fama da ita a kasar, sannan kuma a yi wa kundin zabe gyara.
To sai dai ministan harkokin waje kuma kakakin gwamnati, Abderamane Koulamallah, ya ce ‘yan adawar sun yi wa kansu gurguwar shawara.
Koulamallah ya ce “ƙaurace wa zaben gurguwar dubara ce, saboda haka muke ba su tabbacin cewa za a gudanar da zabe mai tsafta. Bai kamata jam’iyya ta yanke irin wannan shawara ba, ka da su mayar da kansu tamkar ‘yan koyi a fagen siyasa, domin yin hakan zai hana jam’iyyarsu samun nasara”
Ita dai gwamnatin Chadi, tana kallon wannan mataki a matsayin wani yunkuri na yi wa ƙasa bore.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI