Babban bankin na Libya da ke birnin Tripoli shi ne hanya ɗaya tilo da kudaden shigar ƙasar daga cinikin ɗanyen man fetur ke iya isa ga gwamnatocin ƙasar biyu masu faɗa da juna, kuma dakatar da aikinsa zai haddasa gagarumar matsala ga yanayin tafiyar da gwamnatinsu.
Gwamnatocin biyu da suke da fadojin tafiyar da mulki a Tripoli da Benghazi, tsawon shekaru suka shafe suna gwabza fada da juna, duk da cewa babban bankin kai tsaye bai alaƙanta ko ɗaya daga cikinsu da hannu a sace jami’in ba, amma ya bayyana cewa dole sai an sako Mus’ab Muslam ne sannan jami’ansa za su koma bakin aiki.
A cewar bankin wani gungun mutane da ba a san ko su waye ba, su ke da hannu a sace Muslam wanda shi ne shugaban sashen fasahar zamani na babban bankin na Libya.
Sanarwar da bankin ya fitar ya ce ko kaɗan ba zai yi amfani da tsare-tsaren da suka karya doka waɗanda wasu kan yi amfani da su ba, amma zai dakatar da dukkanin ayyukansa har zuwa lokacin da za a sako babban jami’in.
Baya ga sace babban jami’in bankin ya kuma bayyana cewa wasu daga cikin jami’ansa na fuskantar barazana wanda kuma dole mahukuntan da ke mulki a yankunan biyu su shiga tsakani don kawo ƙarshenta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI