Tun farko sojiji da suka karbe iko a wani juyin mulkin da suka yi a shekarar 2021 ƙarƙashin jagorancin Kanal Mamady Doumbouya sun yi alƙawarin mika mulki ga farar hula bayan shirya zaɓe a ƙarshen wannan shekarar ta 2024.
Sai dai kuma tuni mahukuntan ƙasar suka sanar da jinkirta wa'adin saboda bukatar sake fasalin Demokradiyyar ƙasar.
Abdoul Sacko, kodinetan ƙungiyar Forum des Forces Sociales de Guinée, ya ce “babu wata alama da ke tabbatar da cewa shirin mika mulki ga farar hula na kusa daga sojojin dake rike da madufun iko.
Ya soki matakin da ya kira abin takaici tare da yin kira da a gaggauta shirin gudanar da sahihin zaɓe.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI