Ayyukan fasaƙwauri sun sanya Ghana asarar tan dubu 160 na Cocoa a bana

Ayyukan fasaƙwauri sun sanya Ghana asarar tan dubu 160 na Cocoa a bana

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa ayyukan fasaƙwaurin ya kassara hada-hadar Cocoa musamman tsakanin ƙananun manoma waɗanda suka tafka asara a bana, sakamakon yadda kuɗaɗen manoman ke gaza fitowa daga manyan kamfanonin hada-hadar albarkatun wanda ke tilasta su sayarwa ƴan fasaƙwauri a farashi mai rahusa.

A baya-bayan nan anga yadda ayyukan fasaƙwaurin Cocoa ke ta’azzara a Ghana, lamarin da ya sanya ƙasar tafka asarar kimanin kashi 1 bisa 3 na yawan kudaden shigar da ta samu bayan cefanar da Cocoa a shekarar da ta gabata ta 2023.

Shekaru 4 kenan ana samun giɓin yawan Cocoa da duniya ke buƙata sakamakon mummunan yanayin noman albarkatun a ƙasashen Ghana da Ivory Coast wato ta 1 da ta 2 mafiya nomanshi a duniya lamarin da ya jefa tarin kamfanoni a tsaka mai wuya.

Bayanai sun ce an fi ganin hada-hadar Cocoa ta fannin fitar da shi kasuwar duniya a hukumance cikin ƙasashen Ivory Coast da Togo fiye da Ghana a baya-bayan nan, wanda ke da nasaba da ƙaruwar ayyukan ƴan fasaƙwaurin da kuma rashin daidaituwar farashin canjin takardar kuɗi ta CFA.

A bana Ghana ta iya fitar da metric ton dubu 429 da 323 ne tsakanin watan Satumban bara zuwa Yunin shekarar nan ƙasa da kashi 55 cikin ɗari na adadin da ta fitar a bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)