Asusun Maarif ta kasar Turkiyya ta gudanar da taron gwajin kayayyakin kimiyya a Kamaru

Asusun Maarif ta kasar Turkiyya ta gudanar da taron gwajin kayayyakin kimiyya a Kamaru

Gidauniyar Maarif ta Kasar Turkiyya (TMV) ta gudanar da bikin nuna kayayyakin kimiya da al'adu a Yaounde, babban birnin Kamaru.

Bikin da aka gudanar a kwalejin Nkolfoulou na Maarif dake  Yaounde ya samu halartar jakadan Turkiyya a Yaounde Volkan Isıkci, Ministan Ilimin Sakandare na Kamaru Wilfried Gabsa, tsohon firaiminista Philemon Yang da kuma baki da dama.

Isikci yayi jawabin bude taron inda ya bayyana cewa,

"A wannan lokacin  da ake cigaba da fama da Korona har na kusan shekaru biyu, na tabbata cewa wannan sabon karni zai samar da ayyuka da yawa da za su amfani dan adam a fannoni da dama."

Bayan jawabai, bakin sun nishadantu tare da raye-rayen da daliban suka yi na cikin gida da kuma rera wakokin Turkiyya.

Daliban sun nuna bajintarsu ta yin takara da juna a wajen gwada basirarsu akan harkokin kimiyya da al'adu a taron.

A karshen shirin, yayin da bakin suka zagaya wuraren da daliban suka shirya, daliban sun gabatar da ayyukansu ga baki.


News Source:   ()