Ƴan tawayen M23 sun kutsa kai cikin birnin Goma jiya litinin, inda aka yi ta musayar wuta a tashin hankalin da aka kwashe shekaru 30 ana yi, yayin da suka fuskanci tirjiya daga wasu daga cikin sojojin gwamnati.
Kakakin hukumar agajin OCHA Jens Laerke yace ko a yau talata anyi ta jin aman wuta yankin kamar yadda jami'ansa suka tabbatar.
Laerke ya shaidawa wani taron da aka yi a Geneva cewar gawarwakin da aka kai asibitin Goma ya fi karfin cibiyar kula da lafiyar, wanda ke fama da tarin mutanen da suka samu raunuka.
Jami'in ya kuma bayyana samun rahotannin fyade ga mata da kuma 'yan mata daga 'yan tawayen.
Jami'ar hukumar lafiya ta duniya delheid Marschang ta ce an karbi daruruwan mutane a asibiti sakamakon raunukan da suka samu daga harbin bindiga, cikin su harda jami'an kiwon lafiya da kuma jarirai.
Hukumar tace akalla mutane 600 zuwa 700 aka kai asibitin Goma sakamakon raunin bindiga.
Kungiyar agaji ta Red Cross tace daya daga cikin asibitin ta ya karbi mutane sama da 100 a cikin sa'oi 24 sakamakon raunuka daga manya da kananan makamai.
Patrick Youssef, Daraktan kungiyar a Afrika ya ce yayin da suke kula da wadanda suka samu raunukan, suna kuma ci gaba da samun kiraye kiraye ta waya daga mutanen da suka jikkata kuma suke bukatar kai musu dauki.
Mai magana da yawun Hukumar samar da abinci ta majalisar dinkin duniya, WFP, Shelley Thakral ta ce bayan fadan da ake gwabzawa, ana kuma fama da yadda ake fasa shagunan jama'a na sace musu dukiyoyi ciki harda magunguna.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI