
Rahotanni daga Goma na bayyana cewa, asibitin Kyeshero cike yake da majinyatan da suka samu munanan raunuka, inda Prince mungazi, wani mazaunin yankin da aka harba da harsashi ke bayyana cewa, dakarun ‘yan tawaye ne suka harbe shi, bayan sun nemi ya basu kudi, yace musu bashi da ko anini.
‘Yan tawayen M23 dai sun ci gaba da rike ikon birnin Goma tun a makon jiya da suka samu nasarar kwace shi, inda suka ci gaba da fadada mamaayarsu zuwa Kudancin yankin Kivu, kuma suna ci gaba da mamaya ne inda suka nufi babban birnin yankin Bukavu a ranar Juma’a
Goma dai ya kasance wata cibiyar bayar da agaji ga yankin da ke fama da tashe-tashen hankula, inda ake ganin miliyoyin mutane na cikin tsaka mai wuya, bayan da aka samu tsaikon aikin agaji saboda rikici tsakanin ‘yan tawayen da sojojin Congo.
A halin yanzu, babu hanyar kai abinci da magunguna zuwa Goma, saboda tabarbarewar zaman lafiya.
Ma’aikatan jinya sun ce, mutane da dama ne suka samu munanan raunuka, ciki kuwa har da wadanda aka cirewa wani sashe na jikinsu, yayin da suke cikin fargabar rashin kayayyakin kula da majinyata.
A cewar kwararru na Majalisar Dinkin Duniya, ‘yan tawayen na samun goyon bayan dakarun Rwanda kusan 4,000, fiye da wadanda suka taimaka musu a shekarar 2012, wato lokacin da suka kwace ikon Goma na dan gajeren lokaci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI