Ƙasashen yamma sun nemi ficewar jama'arsu daga Congo saboda rikicin M23

Ƙasashen yamma sun nemi ficewar jama'arsu daga Congo saboda rikicin M23

Mahukuntan ƙasashen yammacin 3 sun ce ya zamewa al’ummominsu mazauna Congo wajibi su sauya wurin zama zuwa yankuna masu zaman lafiya tun kafin lokaci ya ƙure musu.

A cewar ƙasashen 3 tun yanzu da iyakoki ke ci gaba da kasancewa a buɗe kuma filayen jirgin sama ke ci gaba da hada-hada shi ne lokaci mafi dacewa na ganin al’ummomin nasu sun fice daga ƙasar mai fama da tashe-tashen hankula.

Rahotanni sun ce Amurka da Faransar da kuma Birtaniya sun aike da saƙon kar ta kwana ne ga al’ummomin nasu ta hanyar wayoyin sadarwa wasu kuma ta sakon email.

Rikici na ci gaba da rincaɓewa tsakanin Sojin gwamnatin Congo da mayaƙan M23 masu samun goyon bayan Rwanda a wani yanayi da Majalisar ɗinkin duniya ke cewa zai iya juyewa zuwa rikicin yanki.

M23 na ci gaba da ƙwace tarin yankuna daga mahukuntan na Congo musamman a lardin arewacin Kivu.

Ko a baya-bayan nan sai da Turkiya ta miƙa tayin shiga tsakani don sasanta rikicin ƙasashen biyu maƙwabtan juna.

Wannan rikici dai na ci gaba da tagayyara al’ummar Congo inda ko a farkon watan nan wasu mutane dubu 230 suka tsere daga matsugunansu saboda fargabar hare-haren ƴan tawayen na M23 a Goma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)