Ƙasashen nahiyar Afrika sun ninka yawan bashin da suke karɓa daga China

Ƙasashen nahiyar Afrika sun ninka yawan bashin da suke karɓa daga China

Daga shekarar 2012 zuwa 2018, Afrika ta karɓi rance na sama da dala biliyan 10  a duk shekara, sakamakon manufar shugaba Xi Jinping na sada nahiyoyin Afrika da Turai ta hanyoyin ruwa da tudu da zummar yauƙaƙa dangantakar kasuwanci, amma sai aka samu koma baya daga a kan rancen tun farkon ɓullar annobar Covid-19 a shekarar 2020.

Binciken wanda cibiyar manufofin bunƙasa ƙasashe ta jami’ar Boston ta gudanar ya nuna cewa an samu ƙarin ninki 3 na basukan da ake samu daga China daga shekarar 2022, abin da ke nuni dacewa ƙasar ta yankin Asiya ta tashi haiƙan wajen kawar da dukkanin  haɗuran da ke tattare da hulda da ƙasashen da bashi ya yiwa katutu.

Cibiyar ta ce china na ci gaba da neman hanyoyin samar da daidaito a tsakanin ƙasashe ta wajen basukan da ta ke bayarwa, kuma tana gwada sabbin dabaru na yin haka.

Binciken ya kuma gano cewa a shekarar da ta gabata, an cimma yarjeniyoyi da suka shafi lamuni har 13 a tsakanin China da ƙasashen Afrika 8.

Waɗannan sabbin alkaluman na zuwa ne  a dai dai lokacin da China ke shirin karɓar baƙuncin jagororin Afrika a mako mai zuwa a taron haɗin kai tsakaninta da nahiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)