A wata wasika mai kwanan 23 ga watan disamba, ministan aikin gona na ƙasar ya ce gwamnati ta kawo ƙarshen kasancewa a cikin shirin majalisar ɗinkin duniya dake tabbatar da wadatuwar abinci a duniya.
Wasiƙar ta zargi shirin na IPC da fitar da rahoto maras tushe dake taɓa ƙima da darajar Sudan.
Ana sa ran wannan kwamiti na majalisar ɗinkin duniya zai fitar da rahoto ƙaruwar bala’in yunwa a sassa 5 na Sudan kuma ana sa ran matsalar ta ƙaru zuwa sassa 10 na ƙasar kamar yadda wata takaddar da Reuters ta gani ta nuna.
A cewar wani shugaban ƙungiya mai zaman kanta dake aiki a Sudan da bai yadda a ambaci sunanshi ba ya ce ficewar Sudan daga shirin zai kawo tsaiko wurin yunkurin da ake na isa ga miliyoyin ƴan Sudan da ke cikin tasku bisa tsanantar yunwa
Ofishin majalisar ɗinkin duniya a birnin New York bai ce komai ba kan wannan mataki da Sudan ta ɗauka na yanke alaƙa da wannan shiri.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI