
A makon da ya gabata ne mayaƙan na M23 suka faɗaɗa mamayarsu zuwa sassan lardin na Kivu bayan da suka ƙwace birnin na Bukavu na biyu mafi girma bayan Goma, a wani yanayi da bayanai ke cewa mayaƙan sun yi amfani da ƙarfi wajen fatattakar fararen hula tare da sace kayayyakinsu, ta yadda ba tare da wani gumurzu ba M23 ta kame birnin.
Bayan da M23 ta ƙwace yankunan na gabashin Congo masu albarkatun ƙarƙashin ƙasa ne, fargaba ta tsananta kan yiwuwar sake faɗaɗuwar yaƙin, lamarin da ya sanya kiraye-kirayen buƙatar janye dakarun da Majalisar Ɗinkin Duniya ke jagoranta a ƙasar.
A birnin na Bukavu, cikin sabon kayan sarki ne ƴansandan suka yi dafifi tare da hawa layi da nufin shiga wani sansanin horaswa na kwanaki don komawa aiki ƙarƙashin dokokin M23.
Bayanai sun ce yawan ƴansandan da suka shiga sansanin samun horon ya kai dubu 1 da 800 waɗanda suka miƙa wuya ga M23. Kodayake kakakin ƙungiyar ƴan tawaye ta AFC Lawrence Kanyuka ya ce akwai kuma wasu ƙarin aƙalla 500 da ke shirin sake miƙa wuya ga M23.
Har zuwa yanzu dai, gwamnatin Congo ba ta tabbatar da miƙa wuyan da waɗannan jami’an ƴan sanda suka yi ga ƴan tawayen ba, kodayake tuni gwamnatin ta sanar da shirin kafa gwamnatin haɗin guiwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI