Annobar cutar ta zazzaɓin mai kamanceceniya da Ebola, na zuwa ne da zazzaɓi mai zafi baya ga haddasa zubar jini daga wasu sassan jiki gabanin kassara aikin gaɓoɓi da kan kwantar da mutum, tuni ta fara yaɗuwa a sassan ƙasar ta Rwanda.
Ministan lafiyar Rwanda Sabin Nsanzimana ya shaidawa taron manema labarai cewa yanzu haka akwai mutane 20 da aka killace waɗanda aka tabbatar sun harbu da cutar ta zazzaɓin Marburg.
A cewar ministan dukkanin mutane 6 da cutar ta kashe kawo yanzu jami’an lafiya ne, kuma tuni aka fara bincike don bin diddigin mutanen da suka yi mu’amala da su gabanin rasuwarsu don killacesu a wani mataki na hanasu yaɗa cutar ga sauran jama’a.
Zazzaɓin Marburg na sahun cutuka dangin ƙwayar cutar filo, wato cutukan da ake kira filovirus irinsu Ebola, cutukan da cikin sauƙi wani kan gogawa wani kuma galibi an fi ganin ɓullar makamantanmsu a ƙasashen Afrika.
Ko a bara anga ɓullar irin cutar a maƙwabciyar Rwanda Tanzania haka zalika anga yadda cutar ta laƙume ɗimbin rayuka a Uganda cikin shekarar 2017.
Binciken masana ya nuna cewa ana samun ƙwayar cutar ne daga jikin wata ƴaƴan itaciya da ake bat, ko da ya ke kai tsaye shan ɗan itaciyar baya saka cuta nan ta ke.
Annobar cutar ta samo sunanta ne daga birnin Marburg na Jamus lura da cewa a can ne aka fara gano ta a jikin wani biri da aka ɗakko daga Uganda cikin shekarar 1967.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI