Annobar Ebola ta sake bulluwa a Guinea tare da kashe mutum hudu

Annobar Ebola ta sake bulluwa a Guinea tare da kashe mutum hudu

Annobar Ebola ta sake bulluwa a kasar Guinea inda ta yi sanadiyar rayukan mutum hudu.

A karshen watan Janairu Ebola ta yi sanadiyar rayuwar wata Nas inda daga bisani aka tabbatar da cewa mutum 8 daga cikin wadanda suka halarci jana'izarta sun kamu da cutar.

Daga cikin su 8 an sanad da cewa uku sun rasa rayukansu.

Ma'aikatar lafiyar kasar ta fara tuntuban dukkanin wadanda suka halarci jana'izar da wadanda suka gana da wadanda suka halarci jana'izar domin daukar matakan da suka dace.

Annobar dake zuwa tare da zazzabi da zubar da jini ta bayyana ne a karon farko a garin Nzara a kasar Sudan da kuma a garin Yambuku dake kasar Jamhoriyar Kongo a shekarar 1976.

Kasancewar Ebola ta fara ne a wani rafi mai suna Rafin Ebola ya sanya aka rada wa cutar suna da hakan.

Annobar Ebola ta yadu dai a Yammacin Afirka a watan Disamban shekarar 2013.

A kasashen Guinea, Laberiya da Saliyo a tsakanin shekarun 2014-2017, mutane dubu 30 sun kamu da cutar kuma fiye da dubu 11 daga cikin marasa lafiya sun mutu.

 


News Source:   ()