An sanar da cewa annobar coronavirus, gurabatar yanayi da farin dango sun kara haifar da matsalar rashin abinci a nahiyar afirka inda miliyoyin al’umma ke fama da rashin abinci.
A Afirka ta yamma ana ganin cewa miliyoyin mutane zasu kasance cikin matsanancin karancin abinci a yayinda da ake fama da Covid-19. A gabashin Afirka an bayyana cewa dokar kullen da aka saka domin magance corona ya jinkirtad da matakan da ake dauka wajen kauda farin dango, musanmman yadda shigowa da maganin kwari zuwa kasashen yankin ya yi wuya
Hakan dai zai kara jefa kasashen nahiyar su kara dogaro ga abincin da ake shigowa dasu daga waje.
Ana hasashen cewa miliyoyin yara ‘yan kasa da shekaru 5 ka iya rasa abincin gina jiki a tsakanin watannin Yuli zuwa Agustaa yankin. Hukumar Samar da Abinci ta duniya (WFP) ta bayyana cewa yawan yaran ka iya dara yawan na bara miliyan 8.2.