Ambaliyar ruwar da ta afku sakamakon cikowar ruwa a rafin Shabe dake kasar Somaliya ya yi sanadiyar yin kauran dubun dubatan mutane sanadiyar nutsewar gidaje da dama a kauyukan dake yankin.
Kafar Talabijin din gwamnati ta SNTV ta rawaito cewa garuruwa da kauyuka da dama sun cika da ruwa sakamakon ambaliyar ruwan da ta afku sanadiyar cikowar ruwa daga rafin Shabe.
Annobar ta yi sanadiyar sanya dubun dubatan mutane yin kaura daga gidajensu inda kuma hukumomi suka yi fadakarwar cewa lamarin ka iya kamari.
Cibiyar Bincike Da Ilimi Ta Majalisar Dinkin Duniya (UNITAR) ta yada wani hoto da bidiyon dake nuna karuwar cikowar ruwan rafin Shabe daga mita 25 zuwa mita 42.
Sanadiyar sauyin yanayi a kasar Somaliya ana yawan samun ambaliyar ruwa da fari, a halin yanzu dai kaso 80 cikin darin kasar na fuskantar matsalar fari.