Ɓangarorin da ke hamayya da juna a Libya sun amince su kafa gwamnatin haɗaka

Ɓangarorin da ke hamayya da juna a Libya sun amince su kafa gwamnatin haɗaka

An yi wannan zaman tattaunawa ne tsakanin ɓangarorin da ke rikici da juna a birnin Bouznika kusa da babban birnin ƙasar Morocco, wato Rabat, inda suka amince su yi aiki a tare ƙarƙashin shirin majalisar ɗinkin duniya, a wani mataki na kawo ƙarshen daɗaɗɗen rikicin siyasa da ke addabar ƙasar.

Tattaunawar dai ta haɗa da majalisar ƙoli ta Libya da ke birni Tripoli a yammacin ƙasar da kuma majalisar wakilai da ke birnin Bengazi a gabashin ƙasar.

Baya ga kafa gwamnatin haɗaka, bangarorin biyu sun kuma amince su aiwatar da sauye sauye a fannonin tsaro da hada hadar kuɗi.

Stephanie Koury da ta kasancce mataimakiyar manzo na musamman a Libya ta shaidawa kwamitin tsaron na majalisar ɗinkin duniya cewa ziyararsu a Libya da ake wa laƙabi da UNSMIL na da nufin kafa kwamitin da zai yi nazari a kan batutuwa da dama, inda aka bayar da wa’adi na kawo ƙarshen matsalolin tare da tsara hanyar shirya gudanar da zabe a kasar. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)