"Mayakan Haftar ba su da niyyar aiki da tsagaita wuta"

"Mayakan Haftar ba su da niyyar aiki da tsagaita wuta"

Rundunar Sojin Libiya ta bayyana cewar 'yan tawaye masu biyayya ga dan juyin mulki Haftar Khalifa ba su da niyyar aiki da yarjejeniyar tsagaita da ke ci gaba da wanzuwa.

Kakakin farmakan Sirte da Jufra Janaral Abdulhadi Dirah ya fadi cewa,

"Mayakan Haftar 'yan tawaye na ci gaba da aiyukan soji. Kullum ana ganin jiragen sama na shawagi a Sirte da Jufra don yin safarar mayaka daga kasashen waje."

Dira ya ci gaba da cewa "Wannan abu da 'yan tawayen na Haftar su ke yi, na nuni da ba su da niyyar aiki da yarjejeniyar 5+5 da ke d manufar kawo karshen yakin da ake yi a Libiya."

Kakakin ya kuma ce, bangaren gwamnatin Libiya na ci gaba da aiki da yarjejeniyar ta Sİrte da Jufra.

A tsakanin 19 da 23 ga watan Oktoban 2020 ne gwamnatin Libiya da mayakan Haftar suka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta hadin kai mai sunan 5+5 don tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a kasar.

A karkashin yarjejeniyar an tanadi cewa, a cikin watanni 3 dukkan sojojin haya za su fice daga Libiya, wannan wa'adi zai kare a ranar 23 ga Janairu.

A karkashin dan tawaye Haftar na Libiya, akwai mayakan Janjawid na Udan, 'yan aksar Chadi, Siriya da kuma dubunnan mayaka na kamfanin Wagner na kasar Rasha.


News Source:   ()