"Kimanin mutum miliyan 9.8 zasu fada cikin matsalar yunwa a Najeriya"

Hukumar Abinci Ta Majalisar Dinkin Duniya (FAO) ta sanar da cewa sanadiyar karancin abinci kimanin mutum miliyan 9.8 na cikin hadarin yunwa a fadin kasar.

Hukumar FAO ta bayyana cewa sanadiyar karancin abinci a jahohi 16 da suka hada da babban birnin Abuja a kallan mutum miliyan 9.8 na cikin hadarin yunwa.

Sanarwar ta kara da cewa jahohin da kungiyar ta'addar Boko Haram ta fi kai hare hare da kuma inda 'yan bindiga ke kai hari da suka hada da Borno, Yobe, Adamawa, Taraba, Katsina, Gombe, Benue da Jigawa ne za'a fi samun matsalar yunwan.

Wadanda kuma zasu biyu a baya sun hada da babban birnin kasar Abuja, Sokoto, Kaduna, Kano, Bauchi, Kebbi, Nijer da jihar Plateau.

Wakilin Hukumar FAO a Najeriya Fred Kafeero, ya yi sharhi akan lamarin inda ya yi kira ga gwamnatin da ta dauki matakan da suka dace cikin gaggawa.

 


News Source:   ()