An sanar da cewa wasu iyan fashın teku sun yı awon gaba da da wasu mutane tara bayan sun kaı hari ga wani jirgin ruwan kasar Norway a yankin tekun Najeriya.
Wani jami'i da ya nemi a sauya sunansa ya bayyana cewa 'yan fashin tekun sun kaiwa jirgin ruwan mai dakon mai hari a yankin Niger Delta.
Yankin tekun Gufl din Guinea dai ya kasance mai hadari sosai sanadiyar yawan harin da 'yan fashin tekun ke kaiwa a yankin.
A bara ma an kaiwa wani jirgin dakon mai hari a yayinda yake kan hanyarsa daga Angola zuwa Togo a inda aka yi gaba da wasu Indiyawa 20.
Haka kuma a watan Yulin bara an kai hari akan jirgin ruwan Turkiyya inda aka kame Turkawa 10 daga cikin 18 domin neman kudion fansa. Jami'an tsaron Najeriya sun kubutar da Turkawan inda suka mikasu ga ofishin jakadancin Turkiyya dake Abuja baban birnin Najeriya.