'Yan tawaye sun kashe fararen hula 16 a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo

'Yan tawaye sun kashe fararen hula 16 a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo

'Yan tawaye masu dauke da makamai sun kai hari tare da kashe fararen hula 16 a kusa da garin Oicha na Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.

Labaran da jaridun kasar fitar na cewa, 'yan tawayen da ke tayar da kayar baya a gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo sun kai hari a kusa da garin Oicha tare da kashe fararen hula 16.

Kungiyar 'yan tawayen mai suna Dakarun Hadin Kan Demokradiyya (ADF) ta kashe a kalla fararen hula dubu 3 daga shekarar 2014 zuwa yau.

Gabashin Jamhuriyar demokradiyyar Kongo na da iyaka da Uganda da Burundi, yanki da tsawon shekaru 20 ake rikici game da zinare da jan karfe a cikinsa inda gwamnati da 'yan tawaye ke kokarin mallakar sa.


News Source:   ()