'Yan ta'addar Boko Haram sun yi garkuwa da ma'aikatan agaji a Najeriya

'Yan ta'addar Boko Haram sun yi garkuwa da ma'aikatan agaji a Najeriya

'Yan ta'addar Boko Haram sun kai hari tare da yin garkuwa da ma'aikatan agaji 7 a arewa maso-gabashin Najeriya.

'Yan ta'addar sun kai wa sojoji hari a yankin Dikwa na jihar Borno.

A yayin kai harin, 'yan Boko Haram sun yi garkuwa da ma'aikatan agaji 7 inda suka kuma kona ofisoshin ma'aikatan agajin.

Jami'in Aiyukan Jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya Edward Kallon ya soki harin inda ya bayyana damuwar da suke da ita game da tsaron lafiya da dukiyoyin jama'ar yankin.

Kallon ya ce, wannan al'amari ya jefa rayuwar kusan mutane dubu 100 da ke bukatar taimakon jin kai a yankin cikin hatsari.

A gefe guda, an kashe mutane 16 sakamakon harin 'yan bindiga a jihar Kaduna.

Kwamishin tsaron Cikin Gida na jihar Kaduna Samuel Aruwan ya shaida cewa, wasu da ba a san ko su waye ba ne suka kai hari da bindigu a yankunan Zangon Kataf da Kurmin Gandu na jihar.

Aruwan ya ce, an kashe mutane 16 tare da jikkata wasu da dama sakamakon harin.

Ya ce, an kuma kona gidaje 10 da babura 2 a harin na 'yan bindiga.

Aruwan ya kara da cewar, an aike da jami'an tsaro zuwa yankunan, kuma an fara gudanar da bincike.


News Source:   ()