'Yan ta'addar Boko Haram sun kashe mutane 75 a Najeriya

'Yan ta'addar Boko Haram sun kashe mutane 75 a Najeriya

'Yan ta'addar Boko Haram sun kai hare-hare a dare guda a yankin arewa maso-gabashin Najeriya inda suka kashe mutane 75.

Labaran da jaridun kasar suka fitar sun rawaito shugaban kwamitin aiyukan soji na majalisar dattawa kuma Sanatan Borno ta Kudu Ali Ndume na cewar, a dare guda 'yan ta'addar sun kashe tsofaffi 75 a yankin Gwoza na jihar.

Ndume ya ce al'umar Gwoza na cikin babban hatsari sakamakon harin na Boko Haram inda ya ci gaba da cewa "Ni a matsayi na na Sanata ba na iya shiga Gwoza saboda babu tsaro. Kowacce rana ana kashe mutane a hare-haren da ake kai wa. Jami'an tsaronmu na yin iya kokarinsu amma al'amuran na da girma sosai. Mutane na mutuwa kowacce rana a nan."

Ndume ya kuma ce baya ga hare-haren, al'Umar yankin na fama da karancin abinci, kuma saboda rashin wanzuwar kungiyoyin farar hula al'amarin na kara munana.


News Source:   ()