Mutane 16 sun rasa rayukansu sakamakon harin ta'addanci da 'yan Boko Haram suka kai a Najeriya.
Jaridun kasar sun bayyana cewa, mambobin kungiyar ta'addar sun kai hari a yankin Rann na jihar Borno.
Mutane 16 da suka hada da soja 1 da wani mai bayar da agaji dan sa kai sun mutu sakamakon harin. Wasu mutanen da dama sun jikkata.