Mutane 44 sun rasa rayukansu sakamakon harin da 'yan ta'addar Boko Haram suka kai wa manoma a arewa maso-gabashin Najeriya.
Tsohon Shugaban Kungiyar Manoma ta Jihar Borno Hassan Zabarmari ya shaida cewar, ma'aikata da ke aikin girbin shinkafa a kauyen Garin Kwashebe na jihar sun gamu da harin 'yan ta'addar Boko Haram.
Zabarmari ya ce, an kashe mutane 44 sakamakon harin inda wasu da dama suka jikkata.