'Yan ta'addar Boko Haram sun kaiwa cibiyar MDD hari a Najeriya

'Yan ta'addar Boko Haram sun kaiwa cibiyar MDD hari a Najeriya

Mutane 5 sun rasa rayukansu sakamakon harin da 'yan ta'addar Boko Haram suka kaiwa cibiyar bayar da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya da ke arewa maso-gabashin Najeriya.

Wani jami'i da ya nemi a boye sunansa ya bayyana cewa, 'yan ta'addar Boko Haram sun kai hari kan cibiyar bayar da taimako ta MDD da ke yankin Damasak na jihar Borno.

Jami'in ya ce, mutane 5 sun rasa rayukansu sakamakon harin.

Sanarwar da Babban Jami'in Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya Edward Kallon ya fitar ta ce, an kaiwa cibiyoyinsu na bayar da taimako 3 hari.

Kallon ya soki harin inda ya ce, jami'an MDD da ke bayar da taimako a yankin na sama da shekaru 10 na fuskantar hare-haren 'yan ta'adda.

Kallon ya shaida cewa, sakamakon hare-haren na Boko Haram za su rage yawan ma'aikatansu da ke yankin wanda hakan zai shafi mutane dubu 8,800 da aka raba da matsugunansu.

 


News Source:   ()