'Yan ta'addar Al-Shabab sun kashe a kalla fararen hula 20 a Somaliya

'Yan ta'addar Al-Shabab sun kashe a kalla fararen hula 20 a Somaliya

An bayyana cewa, a kalla fararen hula 20 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin da kungiyar ta'adda ta Al-Shabab ta kai a Somaliya.

Jami'in dan sanda na yankin Galmudug Muhammad Mahmud ya shaida cewa, bayan an kai harin kunar bakin wake ne aka bude wuta tare da kashe a kalla fararen hula 20.

Kungiyar Al-Shabab kuma ta yi ikirarin kashe jami'an soji 34 a harin.

Kungiyar ta'adda ta Al-Shabab na yawan kai hare-hare kan fararen hula da jami'an tsaro a Somaliya.

A Somaliya da aka dage lokacin gudanar da zabuka, ana ci gaba da kaiwa 'yan ta'addar Al-Shabab farmakai. A 'yan kwanakin nan an kashe 'yan ta'addar kusan 300.

 


News Source:   ()