'Yan ta'addan Boko Haram 91 sun mika wuya a Najeriya

'Yan ta'addan Boko Haram 91 sun mika wuya a Najeriya

'Yan ta'adda 91, mambobin kungiyar ta'adda ta Boko Haram, sun mika wuya a arewa maso gabashin Najeriya.

Mataimakin kakakin ma’aikatar tsaron kasar Najeriya Bernard Onyeuko ya bayyana cewa, mambobin kungiyar 91 sun mika wuya a farmakin da rundunonin soji suka kai a wurare daban -daban a jihar Borno.

Onyeuko ya bayyana cewa an kama makamai da albarusai masu yawa na mambobin kungiyar a farmakin.

Duk dafarmakan da aka gudanar a cikin 'yan shekarun nan, har yanzu kasar Najeriya na fuskantar babbar matsalar tsaro.

Fiye da mutane dubu 20 ne suka mutu a munanan ayyukan tashin hankalin da Boko Haram ta shirya tun daga shekarar 2009 bayan bulluwarta a shekarar 2000.

Tun shekarar 2015, kungiyar ta kuma kai hare -hare a makwabtan kasar Kamaru, Chadi da Nijar. Akalla mutane 2,000 ne suka rasa rayukansu a hare -haren kungiyar a yankin tafkin Chadi.

Dubban daruruwan mutane suka tilastu da yin hijira saboda hare -haren ta'addanci da rikice -rikice a kasar.


News Source:   ()