'Yan Najeriya kimanin dubu 5 da suka gudu Kamaru saboda rikicin 'yan ta'addar Boko Haram sun koma matsugunansu.
Wani jami'in sadarwa a Najeriya Malam Isa Gusau ya shaida cewa, ta hanyar hadin kan gwamnatin Kamaru da ta jihar Bornon Najeriya, 'yan Najeriya dubu 5 da suka gudu Kamaru tare da neman mafaka saboda hare-haren Boko Haram sun koma garuruwansu.
Gusau ya ce, mafi yawan wadanda suka dawo din sun gudu ne daga sansanin 'yan gudun hijira na Minawo a shekarar 2014 zuwa Kamaru.
Akwai 'yan Najeriya sama da dubu 60 da ke gudun hijira a Kamaru.