'Yan juyin mulki da suka karbe mulki a kasar Mali a ranar 18 ga Agusta na ci gaba da yin nade-nade a gwamnati.
Sanarwar da Majalisar Kasa ta Kubutar da Al'uma ta fitar a jaridar gwamnati na cewa an nada Oumar Diarra a matsayin Shugaban Rundunar Sojin Mali.
An nada Souleymane Doucoure a matsayin Sakatare Janar na Ma'aikatar Tsaro, inda ganin an samu fararen hula 2 a cikin kunshin jami'an ya ja hankali sosai.
Shugaban 'yan juyin mulkin Assimi Goita ya nada Cheick Oumar a matsayin kakakinsa, sai Youssouf Coulibaly a matsayin mai ba shi shawara kan harkokin shari'a.