Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewar, sakamakon annobar Corona (Covid-19), 'yan gudun hijira kimanin miliyan 1,3 ne suke fuskantar karancin abinci a kasar Uganda.
Daraktan Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya Al-Khidir Daloum ya shaida cewa, wannan matsala ta karancin abinci ta fi shafar mata da yara kanana.
Dalum ya kara da cewa "Sakamakon raguwar taimako da ake bayarwa, 'yan gudun hijira miliyn 1,26 na fuskantar matsalar rashin isasshen abinci a Uganda."
Daloum ya kuma ce, akwai 'yan gudun hijira daga kasashen Burundi da Sudan ta Kudu a Uganda, kuma bai kamata annobar Corona ta zama hujjar da za ta sanya kasashen duniya su juyawa 'yan gudun hijira baya ba.
Kasar Uganda da ke gabashin Afirka ce kasar da ta fi kowacce karbar 'yan gudun hijira nahiyar.