A kalla 'yan gudun hijira 20 ne suka rasa rayukansu sakamakon jefa su teku da masu fataucin mutane suka yi a Djibouti.
Rahotanni sun ce, masu fataucin mutanen sun jefa 'yan gudun hijira kimanin 80 a gabar tekun Djibouti.
Daraktan Hukumar Yaki da Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya a Gabashin Afirka Muhammad Abdikar ya fitar da sanarwa ta shafinsa na Twitter inda ya ce, an jefa 'yan gudun hijira 80 teku daga cikin wani jirgin ruwa da ke hanyar zuwa Yaman inda 20 daga cikin su suka rasa rayukansu.
Abdikar ya shaida cewa, dubunnan 'yan Afirka ne ke kokarin isa kasashen Gulf ta jiragen ruwa, kuma wannan ne ibtila'i na 3 da aka fuskanta a watanni 6 da suka gabata inda sama da mutane 70 suka rasa rayukansu.
Masu fataucin mutane na yawan jefa 'yan gudun hijira teku sabpoda tsoron jami'an tsaro da za su iya kama su.