'Yan gudun hijira ba bisa ka'ida ba 74 ne suka rasa rayukansu sakamakon kifewar da jirgin ruwansu ya yi a gabar tekun Libiya.
Hukumar Yaki da Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (IOM) ta bayyana cewar akwai mutane sama da 120 da suka hada da mata da yara kanana a cikin jirgin ruwan.
An bayyana cewar a kalla mutane 74 ne suka mutu sakamakon kifewar, kuma masunta da jami'an tsaron teku sun fitar da mutane 74 da aka kubutar zuwa gaba.
An bayyana cewar ana ci gaba da neman mutanen da suka dilmiye inda ya zuwa yanzu aka samu jikkunan mtane 31.
Daraktan IOM na Libiya Federico Soda, ba tare da ambatar suna ba ya soki kasashen Turai inda ya ce "Mutanen da ba su da katabus na ci gaba da halaka ta hanyoyin ruwa da na kasa."
Alkaluman IOM sun bayyana cewar a wannan shekarar 'yan gudun hijira ba bisa ka'ida ba 900 ne suka dilmiye tare da rasa rayukansu a tekun Bahar Rum.