A kalla 'yan gudun hijira 43 ne suka rasa rayukansu sakamakon kifewar jirgin ruwan da suke ciki a tekun Bahar Rum.
Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa, a kalla mutane 43 ne suka rasa rayukansu sakamakon kifewar jirgin a tekun Bahar Rum, an samu nasarar kubutar da wasu mutane 10.
Libiya na kan gaba a tsakanin hanyoyin da 'yan Afirka ke bi don zuwa Turai da nufin neman rayuwa ingantacciya.