'Yan gida daya 24 sun mutu sakamakon cin takin zamani a cikin abinci a Najeriya

'Yan gida daya 24 sun mutu sakamakon cin takin zamani a cikin abinci a Najeriya

A jihar Sokoto da ke Najeriya, mutane 24 daga iyali daya sun rasa rayukansu sakamakon takin zamani da aka saka a cikin abincin da suka ci bisa kuskure.

Kwmishinan lafiya na jihar Sokoto Dr. Ali Inname ya shaida cewa, a kauyen Danzanke na jihar an yi amfani da takin zamani a madadin gishiri a cikin abinci inda mutane 24 daga iyali daya suka mutu.

Inname ya kara da cewa, waus mutanen 2 kuma na karbar kulawa a asibiti.

Ya ce, ya zama wajibi mutane su dauki darasi daga wannan abu tare da nisantar da gidajensu da kayayyaki masu sinadaran da ka iya kisa domin hana sake afkuwar hakan a nan gaba.

Inname ya bukaci duk wadanda suka ji ba sa jin dadi da ke yankin da su ziyarci asibiti.


News Source:   ()