Akalla mutane 35 ne suka mutu wasu da dama suka jikkata a wani hari da makami da aka kai a jihar Zamfara da ke Najeriya a Yammacin Afirka.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Zamfara Mohammed Shehu ya ce, 'yan bindiga sun kai harin ramuwar gayya a gundumar Maradun da ke lardin a ranar Alhamis.
Shehu ya ce mutane 35 suka rasa rayukansu yayin da da dama suka jikkata a hare-haren.
A gefe guda kuma, rahotannin kafofin yada labaran cikin gida sun yi ikirarin cewa mutane 39 sun rasa rayukansu a hare-haren.
An kashe wasu gungun 'yan daba biyu a cikin samamen da jami'an tsaron yankin suka yi wa mutane dauke da makamai a ranar 7 ga watan Yuli.