Mutane 12 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin da 'yan bindiga suka kai a tsakiyar Najeriya.
Labaran da jaridun Najeriya suka fitar na cewar wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba ne suka kai hari a jihar Kogi da ke arewa ta tsakiyar kasar.
Mutane 12 sun mutu sakamakon harin, wasu da dama sun jikkata.
A gefe guda Kakakin Ma'aikatar Tsaron Najeriya John Enenche ya bayyana cewar sun kai wa 'yan bindiga farmakai a jihar Bayelsa.
Enenche ya ce an kassara 'yan bindiga 6 a farmakan, kuma an kwace makamai da dama daga hannaunsu.