A wani harin da 'yan bindiga suka kai a yankin Birnin Gwari mutun 23 sun rasa rayukansu.
Kamar yadda shugaban yan sandan jihar Kaduna Samuel Aruwan ya bayyana wasu da ba'a san ko su wanene ba sun kai harin bindiga a yankunan Birnin Gwari, Giwa, Chikun, Igabi da Karu.
Aruwan ya bayyana cewa a hare haren mutane 23 sun rasa rayukansu inda wasu da dama suka raunana.
Aruwan ya Kara da cewa an aike da jami'an tsaro yankin domin inganta tsaro.