'Yan bindiga sun hallaka mutane 14 a jihar Sokoto dake Najeriya

'Yan bindiga sun hallaka mutane 14 a jihar Sokoto dake Najeriya

An sanar da kai wani harin bindiga a jihar Sokoto dake Najeriya wanda ya yi sanadiyar rayukan mutane 14

A wani kauye mai suna Tara ne aka kai hari da bindiga inda mutane 13 suka mutu nan take kuma wasu da yawa sun raunana.

Kamar yadda rundunar yan sandan jihar ta sanar a yankin Dingyadi ma an kai harin da aka yi sanadiyar rayuwar mutum daya.

Kasancewar yadda ake yawan kai hare-haren bindiga saman bubura an kashe mutane a kasar ta Najeriya ya sanya haramta amfani da bubura a wasu jahohin kasar.

A yankin dai ana yawan samun rikici tskanin makiya da manoma, a kwanakin baya ma an kai harin da ya yi sandiyar rayukan mutane 19.

 


News Source:   ()