An sanar da cewa a wani hari da 'yan bindiga dadi suka kai a wajen hakar zinare dake jihar Zamfaran Najeriya mutum 22 sun rasa rayukansu.
Kamar yadda kafafen yada labaran cikin gidan kasar suka rawaito a yankin Dankurmi dake jihar wasu 'yan bindiga dadi sun kai hari saman babura inda suka kama harbi kan mai uwa da wabi.
A harin mutum 22 sun rasa rayukansu inda kuma wasu da yawa suka raunana.
Jihar Zamfara dai ta kasance cikin tsawon shekaru 5 ta na fama da rikici tskanin makiyaya da manoma.