Mutane 7 sun rasa rayukansu sakamakon hare-haren 'yan bindiga da aka kai a wurare biyu daban-daban a Najeriya.
Kwamishin Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar Kaduna Samuel Aruwan ya shaida cewa, wasu da ba a san ko su waye ba ne suka kai hare-hare da bindigu a yankunan Kakau da Tsohon Gaya da ke jihar.
Aruwan ya shaida an kasshe mutane 7 tare da jikkata wasu da dama sakamakon hare-haren.
Sakamakon yadda ake yawan kai hare-hare a kan babura a arewacin Najeriya wasu jihohi suka haramta hawa babur gaba daya.