A makon nan, 'yan adawa a fadin kasar Sanagal za su ci gaba da zanga-zangar da suka fara bayan kama madugun 'yan adawa kuma shugaban jam'iyyar PASTEF Ousmane Sonko.
Gamayyar Jam'iyyun Adawa da na Kungiyoyin Farar Hula da suka kafa Gwagwarmayar Kare Demokradiyya sun gudanar da taron manema labarai a Dakar Babban Birnin Sanagal.
Cheikh Tidiane Dieye ya yi jawabi a madadin Gwagwarmayar inda ya ce, daga ranar Litinin din nan za a gudanar da zanga-zangar ta kwanaki 3 a fadin Sanagal don nuna adawa ga gwamnatin Shugaba Macky Sall.
Wani mamban Gwagwarmayar mai suna Yassine Fall ya yi kira da a gaggauta sakin Sonko, kuma akwai bukatar a gudanar da bincike a matakin kasa da kasa game da wadanda aka kashe a yayin zanga-zangar.
Labaran da jaridun Sanagal suka fitar sun ce, ya zuwa yanzu an kashe mutane 6 a zanga-zangar kin jinin gwamnati da ake yi.
A ranar 3 ga Maris aka fara zanga-zanga a Sanagal bayan kama madugun 'yan adawa Sonko da jami'an tsaro suka yi.
Kalaman da dan adawar ya dinga yi a kwanakin baya na sukar wanzuwar Faransa da kamfanoninta a Sanagal sun janyo mutane sun nuna bacin ransu a kan shagunan Faransawa.
Bata gari sun farwa shagunan kamfanin Auchan na Faransa tare da kwashe kayayyaki da kona su. Haka zalika kamfanin Orange na Faransa ya rufe dukkan cibiyoyinsa har zuwa lokacin da zai fitar da sanarwa.
Haka zalika a wani dakin tausa da ke Dakar Babban Birnin Sanagal, wata mai shekaru 20 Adji Sarr ta zargi Sonko da yi mata fyade, kuma ya yi zargin kashe ta, wanda hakan ya bayyana ne bayan ta kai kara kotu.