Bayan da aka sanar da nasarar Mohamed Bazoum a zaben Shugaban Kasar Jamhuriyar Nijar, dan takarar jam'iyyar adawa Mahamane Ousmane ya yi korafi game da hukuncin kotun koli.
Labaran da jaridun Nijar suka fitar na cewa, Ousmane ya yi korafi game da hukuncin da kotun koli ta fitar na cewa, dan takarar jam'iyyar PNDS-Tarayya Bazoum ya samu kaso 55,66 na kuri'un da aka jefa.
Sanarwar da Ousmane ya fitar ta shafin Facebook ta yi kira ga magoya bayansa da su gudanar da zanga-zangar lumana.
Kotun kolin Nijar a ranar Litinin din nan ta sanar da cewa, dan takarar jam'iyyar RDE-Tchanji kuma tsohon Shugaban Kasa mai shekaru 71 Ousmane ya samu kaso 44,34 na kuri'un da aka jefa a zagaye na 2 zaben.
A ranar 27 ga Disamban 2020 aka yi zagaye na farko na zaben, inda aka gudanar da zagaye na 2 a ranar 21 ga Fabrairu.
Shugaban Kasar Nijar na yanzu Mohammadou Issoufou bai iya sake tsayawa takara ba saboda kammala wa'adinsa na zango 2 da ya yi.