Jam'iyyar 'Yanci da Cigaba ta 'Yan adawa a Chadi ta soki yadda aka nada dan tsohon Shugaban Kasar Idris Deby da aka kashe a filin yaki a matsayin magajin mahaifinsa, inda ta bukaci da a mika mulki ga farar hula nan take.
Sakataren jam'iyyar Muhammad Ahmad Al-Habu ya ce, kundin tsarin mulki ya tanadi idan babu Shugaban Kasa to Shugaban Majalisar Dokoki ne zai hau mulki.
Ya ce "Wannan juyin mulki ne ga kundin tsarin mulki, muna sukar nadin shugaban da aka yi."
A gefe guda, gwamnatin rikon kwarya ta soji ta Chadi ta bayyana cewa, an bude dukkan iyakokin kasa da na sama da aka rufe a kasar, kuma za a koma gudanar da aiyuka yadda su ke a baya.
Haka zalika an bayyana sassauta dokar hana fita waje daga karfe 18.00 zuwa 08.00.