Kungiyar 'yan a ware da ke tayar da kayar baya a Chadi ta bayyana ba ta amince da sabuwar gwamnatin rikon kwarya ta soji da aka kafa a kasar ba.
Kakakin Kungiyar FACT ta 'yan a ware da ta ke kai hare-hare a Chadi Kingabe Ogouzeimi de Tapol ya fitar da sanarwar cewa, Chadi ba masarauta ba ce da dan zai gaji ubansa a kujerar mulki, kuma ba su amince da gwamnatin soji ta rikon kwarya da aka kafa ba.
Ogouzeimi de Tapol ya ce,
"Ba ta hanyar kada kugen tsana da wariya za su shiga Ndjemena ba, da zaman lafiya da sauyi za su shiga birnin."
A karshen makon da ya gabata ne aka jikkata Shugaban Kasar Chadi yayin fafata rikici da 'yan tawaye a arewacin kasar, kuma ya mutu a ranar 20 ga Afrilu.
Jim kadan bayan mutuwar sa aka nada dansa wanda shi ne Kwamandan Dakarun tsaron Fadar Shugaban Kasar Chadi Janaral Mahamat Idris Deby a matsayin Shugaban gwamnatin soji ta rikon kwarya.
A shekarar 2016 ne Mahamat Mahdi Ali ya kafa kungiyar FACT ta siyasa da soji a Chadi.
'Yan a waren sun fito daga kabilar Gorani ta tsohon Shugaban Kasar Chadi Hissene Habre, kuma sun fara yaki ta hanyar bayar da gudunmowa ga mayakan Misrata da ke yaki da 'yan tawayen Haftar da Daesh a Libiya.
A ranr 11 ga Afrilu da ake gudanar da zaben Shugaban Kasar Chadi FACT ta kai hari a arewacin kasar.
A makon da ya gabata rundunar sojin Chadi ta fara kaiwa 'yan tawayen farmakai.