Ana zargin sojojin Mali da na Wagner da kashe fararen hula 20

Ana zargin sojojin Mali da na Wagner da kashe fararen hula 20

Wani makusancin matukin, wato guda daga cikin motocin da aka kai wa harin daga birnin Gao na arewacin ƙasar, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, lamarin ya faru ne lokacin da gungun dakarun ke kan hanyar zuwa Aljeriya.

A cikin wata sanarwa da rundunar tsaron Mali ta fitar ta bayyana cewa, sun samu nasarar kashe 'yan ta’adda 7 tare da kwato makamai da dama.

Haka zalika, rundunar ta ce an samu arangama a lokuta mabanbanta da ƙungiyoyin masu dauke da makamai a yankin na arewacin Mali.

Amma wata majiyar tsaro ta ƙaryata zargin kai harin a baya, inda ta ce su na gudanar da bincike amma dakarunsu basu kashe koda mutum guda ba.

Mali wadda aka samu juyin mulki a jere a shekarun 2020 da 2021, ta shafe gomman shekaru ta na fama da matsalolin tsaro sakamakon rikicin  ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi da ke da alaƙa da Al-Qaeda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)