Ana zargin sojojin Chadi da kashe ƴan Najeriya da ke kamun kifi

Ana zargin sojojin Chadi da kashe ƴan Najeriya da ke kamun kifi

Sojojin na Chadi sun ƙaddamar da farmaki ne a tsibirin Tilma da ke Kukawa a kusa da Tafkin Chadi a ranar Larabar da ta gabata, a dai dai lokacin da masunta ke kamun kifi a cikin ruwa.

Majiyoyi guda 2 da ke taimaka wa sojojin Najeriya wajen yaƙi da Boko Haram sun tabbatar da labarin ga Kamfanin Dillancin Labaran AFP, inda suka shaida massa cewar masunta da dama sun mutu sakamaon harin.

Ɗaya daga cikinsu Babakura Kolo ya ce jirgin soji na yaƙi ne mallakar Chadi ya yi ruwan wuta a kan masuntan a tsibirin Tilma, kuma da dama daga cikin su sun sheka lahira.

Kolo ya ce jirgin ya ɗauka masuntan mayakan Boko Haram ne da suka kai hari a kan dakarun ƙasar Chadi, saboda haka ya kai musu wannan hari cikin kuskure.

Wani babban hafsan sojin Chadi mai rike da muƙamin Janar da ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da kai hare-haren a kan tsibirin da ke kan iyakar Najeriya da Nijar.

Sau tari mayakan Boko Haram kan saje da masu sana’ar kamun kifi da kuma manoma bayan sun kai hari domin badda sawu.

Shugaban ƙasar Chadi Mahamat Idris Deby da kansa ya yi alƙawarin farautar mayakan domin murƙushe su bayan ya ziyarci barikin sojin da aka hallaka wasu dakarunsu.

Akasarin masuntan da harin ya rutsa da su sun fito ne daga garin Baga da Doron-Baga da kuma Duguri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)