Ana zargin Rundunar Sojoji Mali da dakarun Wagner da kisan gilla a Douentza

Ana zargin Rundunar Sojoji Mali da dakarun Wagner da kisan gilla a Douentza

 

Baya ga asara ta dukiyoyi ,rundunar hadin guiwar sojin kasar Mali (Fama) da kungiyar Wagner ta kasar Rasha sun aikata wani sabon kisan kiyashi a yankin Douentza a tsakiyar kasar a cikin mako inda suka bar garin Koro zuwa Boulikessi a ranar Talata 21 ga watan Janairu.

Bayanan da aka samu daga mazauna yankin da wakilan al’umma da dama na cewa, an fara sace mutane yan kabilar dogon uku daga yankin Dinangourou, sannan aka gano gawarwakinsu a yanke kawunansu.

 Hotunan da aka aika zuwa RFI da ban tausayi.

Sojojin kasar Mali Sojojin kasar Mali AFP - BOUREIMA HAMA

Rahotanni na nuni cewa washegari, ranar Laraba, 22 ga watan Janairu, mutanen Wagner da sojojin Mali sun kashe Fulani biyar tare da harbe wasu hudu tare da kuma raunata wasu hudu a kauyen Bouldé, da ke karkashin ikon Mondoro.

Wadanda abin ya shafa sun kai shekaru 14 zuwa 73. Majiyoyin RFI sun bada rahoton kutsawa cikin iyalai da misalin karfe 8 na safe, inda aka tsaga maƙogwaron mutane a gidajensu, an kona rumbunan gero kusan arba'in da kuma lalata babura da dama.

Ya zuwa wanan lokaci,hukumomin sojin kasar ta Mali ba su ce ufon ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)