Ana zargin bullar cutar ƙyandar biri a jamhuriyar Nijar

Ana zargin bullar cutar ƙyandar biri a jamhuriyar Nijar

Babban magatakarda a ma'aikatar lafiyar Nijar Dakta Malam Ekoye Saidou wanda ya tabbatar da matakin cikin wata sanarwa ranar Laraba, ya buƙaci masu ruwa da tsaki a kowane mataki da su ƙarfafa matakan taka tsantsan a duk wuraren kiwon lafiya na gwamnati da masu zaman kansu da kan iyakoki.

Sanarwar tace ɗaukar matakin ya zama dole, sakamakon yadda cutar ta fara yaɗuwa zuwa yammacin Afirka.

Daga ranar 14 ga watan Agusta, mutane 833 ne suka kamu da cutar, ciki har da 9 da su ka mutu a yankin, wato 11 a Najeriya, 1 Ivory Coast da kuma 3 a Benin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)