Suleiman Waziri a ranar Talata, dan uwan ga shugaban kungiyar , ya bayyana cewa an kama Badejo ne bisa wani abu da ya faru da wani Janar mai ritaya a Tudun Wada, karamar hukumar Karu, a ranar 8 ga watan Disamba, 2024.
Waziri ya ce Badejo, wanda ba shi da hannu a lamarin, an kai shi ne saboda yunkurin sasanci a matsayinsa na shugaban al’umma da ake girmamawa.
A garin Tudun Wada, karamar hukumar Karu, jihar Nasarawa,ranar 8 ga watan Disemba wani Janar na Sojojin Najeriya mai ritaya, ya yi harbi da bindiga a kan garken shanu, lamarin da ya janyo hasarar makiya. Da yake kare kansu, makiyayan sun kwance wa Janar din makamai tare da kai karar ga ‘yan sanda.
“Duk da cewa ba shi da alaka da wannan lamarin, an kama Alhaji Bello Badejo ne a ranar 9 ga watan Disamba 2024 a ofishinsa da ke Maliya, Jihar Nasarawa, a wani samame da Bataliya ta 117 ta kai.
Rahotanni na bayyana cewa Sarkin ba shi da alaka da abin da ya faru a Tudun Wada. Suleiman ya karasa da cewa "shi kawai dan uwana a cikin wannan lamari ya taso ne lokacin da 'yan uwan makiyayan suka tunkare shi da safiyar ranar 9 ga watan Disamba, 2024, inda suka roke shi da ya shiga tsakani a matsayinsa na shugaba mai daraja don ya taimaka wajen ganin an sako shanunsu da aka kwace."
Waziri ya koka da irin yadda dan uwansa ya yi, ciki har da kin samun lauyoyi da kuma ‘yan uwa.
“Kokarin da jami’an lauyoyin mu suka yi na ganinsa ya ci tura daga bataliya ta 117.
Iyalan sun yi kira ga babban hafsan soji da sauran hukumomin da abin ya shafa da su gaggauta sakin Badejo ba tare da wani sharadi ba.
Mukaddashin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, Laftanar Olokodana Odunayo, ya tabbatar wa manema labarai cewa an mayar da Badejo zuwa hukumar leken asiri ta hukumar DIA.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI