Jami'ai a N'djamena sun ce zaɓen na wannan Lahadi zai kawo ƙarshen majalisar rikon kwarya ta soji na shekaru uku, wanda ya samo asali bayan mutuwar tsohon shugaban ƙasar Idriss Deby Itno a shekarar 2021 wanda ɗansa, Mahamat Idriss Deby ya gada, kuma aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa na mulkin farar hula a watan Mayun 2024.
Tun a ranar Asabar sojoji da mutanen da za su yi aikin zaben, da kuma ƴan Chadi mazauna ƙatare suka ƙada ƙuri’unsu.
Sama da sojoji 45,000 a fadin ƙasar ne aka yi kira su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI